Home Sabon Labari Buratai da sauran tsoffin hafsoshin soji sun zama sabbin jakadun Nijeriya

Buratai da sauran tsoffin hafsoshin soji sun zama sabbin jakadun Nijeriya

75
0

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya nada tsofaffen shugabannin sojin kasar da ya sauke a kwananan a matsayin jakadun kasar (ambasada) a ketare.

Mai ba shugaban shawara ta bangaren yada labarai Femi Adesina a cikin sanarwar da DCL Hausa ta samu a wannan Alhamis ya ce tuni shugaban Nijeriyar ya tura sunayen Janar Buratai da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas da AM Sadique Abubakar masu murabus zuwa ga majalisar dattawa domin a tabbatar da nadin da aka yi musu na jakadun Nijeriya da za a tura su kasashen ketare don su wakilci kasar a harkar diflomasiyya.

Sanarwar da ba ta baiyana kasashen da za tura su Buratai din ba, ta hada sunan Air Vice Marshal Mohammed S. Usman mai murabus da shi ma shugaban Nijeriyar ya nada a matsayin ambasada.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply