Home Labarai Buhari ya roƙi kamfanoni su ɗauki matasa aiki

Buhari ya roƙi kamfanoni su ɗauki matasa aiki

93
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga bangarori masu zaman kansu a fadin jihohin Nijeriya da Abuja, su dauki matasan kasar aiki a kamfanoninsu.

Shugaban kasar ya yi wannan kiran ne a birnin Abakiliki ranar Litinin, lokacin kaddamar da shirin samar da aiki na musamman da gwamnatin tarayya ta yi.

Buhari wanda ya samu wakilcin Ministan Kimiyya da Fasaha Dr. Ogbonnaya Onu, ya yi bayanin cewa manufar kirkiro da shirin samar da aikin na cikin kokarin gwamnatinsa na magance matsalolin da cutar Covid-19 da EndSARS ta haddasa a kasar.

A nasa jawabin shugaban samar da aikin na jihar Ebonyi Dr. Edward Nkwegu ya ce gwamnatin tarayya za ta kashe kimanin Naira miliyan 780 a cikin watanni uku don aiwatar da shirin a cikin jihar Ebonyi kadai.

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply