Home Labarai Buhari ya saɓa alƙawarin halartar zaman majalisa

Buhari ya saɓa alƙawarin halartar zaman majalisa

143
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki amsa gayyatar da majalisar wakilai ta yi masa a ranar Alhamis dinnan.

A ranar 1 ga watan Disamba ne dai majalisar ta gayyaci Buhari domin ya yi mata bayani kan matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta.

Haka ma, mai taimakawa shugaban kasar kan kafafen intanet Lauretta Onochie ta tabbatar da cewa Buharin zai halarci zaman majalisar na ranar Alhamis, kafin Ministan Shari’a Abubakar Malami ya fito ranar Laraba ya kalubalanci gayyatar, yana mai cewa majalisar ba ta da ‘yancin gayyatar Buhari.

A kan haka ne kuma, shugaban kasar bai halarci majalisar ba a zamanta na yau Alhamis kamar yadda aka tsara.

Da yake magana kan rashin halartar shugaban kasar, wani dan majalisa daga jihar Rivers Solomon Bob, ya bukaci shugaban majalisar Femi Gbajabiamila ya yi wa ‘yan majalisar bayanin halin da ake ciki kan batun.

Da yake maida jawabi, Gbajabiamila, ya ce majalisar za ta jira bayani a rubuce daga bangaren shugaban kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply