Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin sabuwar dokar gudanar da harkokin banki da ma sauran cibiyoyin da ke hada-hadar kudade wato BOFI 2020.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimakawa Shugaban kasar fannin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa sabuwar dokar ta BOFI za ta kawo gagarumin sauyi mai ma’ana fannin tafiyar da cibiyoyin na hada-hadar kudade ta yadda za a kara inganta tattalin arzikin kasa.
