Home Labarai Buhari ya tura dakarun soji da ƴansanda don ceto ƴan makarantar Kagara

Buhari ya tura dakarun soji da ƴansanda don ceto ƴan makarantar Kagara

43
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura tawagar sojoji da ‘yansanda zuwa jihar Neja domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su a makarantar Sakandiren Kimiyya ta Kagara.

Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Garba Shehu ya fitar ranar Larabar nan, Buhari ya bukaci a ceto wadanda aka sacen cikin gaggawa.

Jami’an tsaron za su gana da jami’an gwamnatin jihar, shugabannin al’umma, iyayen yara da ma’aikatan kwalejin, domin shirya yadda za a ceto mutanen.

Haka kuma, Gwamnan jihar Abubakar Sani Bello ya ce gwamnatinsa ba za ta biya ko sisin kobo a matsayin kudin fansar ceto daliban da aka sace a kwalejin kimiyyar da ke Kagara.

Bello ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da ‘yanjarida a ranar Larabar, biyo bayan sace dalibai da ma’aikatan Kwalejin a tsakar dare.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply