Home Labarai Buhari ya umarci a fara biyan sabon tsarin albashin ƴan sandan

Buhari ya umarci a fara biyan sabon tsarin albashin ƴan sandan

261
0

Shugaba Buhari, ya umarci hukumar kula da tsara albashi ta Nijeriya, ta hanzarta daddale sabon tsarin albashin ƴan sandan ƙasar.

Shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a jawabinsa na yammacin ranar Alhamis, yana mai umartar hukumar ta hanzarta aiwatar da sabon tsarin.

Ya ce ana kuma yin bitar albashin sauran hukumomin tsaron ƙasar.

Buhari ya ce an saurari ƙudirori biyar da masu zanga-zangar EndSARS suka gabatar kuma an aiwatar da su, wanda tabbatar da walwalar ƴan sandan yana ciki.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply