Shugaba Buhari ya dawo Nijeriya bayan ya kwashe fiye da kwanaki 10 ba ya kasar. Jirgin da ya kawo shi ya sauka a filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja da misalin karfe 9.40 na dare a ranar Juma’a.
Tun da farko dai an tsara shugaban zai kasance a birnin Landan daga 02.11.2019 zuwa 17.11.2019. Amma kuma sai ga shi ya dawo ranar Juma’ar nan 15.11.2019.


Wasu sun fara alakanta wannan yanke hutun da nasarar da kotun kolin Nijeriya ta ba shi a shari’ar zaben shugaban kasa da ta biyo bayan zaben watan Fabrairu.
Sai dai mai magana da yawun shugaba Buhari Femi Adeshina bai bayyana dalilin yanke hutun da shugaban ya yi ba. Amma ya sanya hutunan dawowar shugaban a shafinsa na Facebook.
