Home Labarai Buhari ya yi takaicin yadda ake mallakar makamai barkatai

Buhari ya yi takaicin yadda ake mallakar makamai barkatai

167
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana farin cikin sakin daliban makarantar sakandiren Kankara a jihar Katsina da aka yi.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar a daren Alhamis, Buhari ya bayyana sakin daliban a matsayin wani abu da zai dawo da kwanciyar hankali ga iyaye, kasa da ma duniya baki daya.

Shugaban kasar ya bayyana takaicin yadda ‘yan bindigar suke cigaba da mallakar makamai duk da rufe iyakokin kasar da aka yi na tsawon lokaci, ya kuma sha alwashin magance matsalar ta ta’addanci.

Buhari ya yaba wa kokarin jami’an soji da na ‘yansanda, da kuma gwamnatin ta Katsina da ta Zamfara bisa yadda suka hada kai don ganin an ceto rayuwar daliban.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply