Home Addini Buhari ya yi tir da rikicin Oyo

Buhari ya yi tir da rikicin Oyo

44
0

Shugaban Nijeriya Muhammad Buhari yace gwamnatinsa za ta cigaba da kare mutunci addini da kabilun kasar kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.

A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawunsa Garba Shehu a Abuja, shugaba Buhari ya yi tir da Allah wadai da wadannan hare-hare.

DCL Hausa ta ba da rahoton cewa Shugaba Buharin na mayar da martani ne kan wasu rikice-rikicen kabilbanci da suka taso a wasu sassan kasar. Ya ja kunnen cewa gwamnati ba za ta rike hannu ta zura ido tana kallon wannan bahallatsar na faruwa ba.

Ya yi kira ga gwamnoni da iyayen kasa da shugabannin addini da su hada hannu da gwamnatin tarayya don tabbatar da ba a samun barkewar rikice-rikice a yankunansu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply