Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya zargi shugabannin al’umma a jihar Borno da rashin ba jami’an soji haɗin kan da ya dace ga yaƙi da Boko Haram a jihar.
Buhari ya ce babu yadda za a yi ƴan ta’addar su shirya kuma su aiwatar da hari ba tare da shugabannin suna da msaniya ba.
Shugaban ya faɗi haka ne lokacin da yake maida jawabi a kalaman da Shehun Borno da kuma gwamnan jihar suka yi kan matsalar ƴan ta’addan.
A jiya ne da Buharin ya kai ziyarar jajantawa, kwanaki kaɗan bayan wani harin ta’addanci da ya yi silar mutuwar sama da mutum 30 a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.
A lokacin ziyarar dai, jama’ar jihar sun nuna ɓacin ran su kan yadda gwamnatin Buhari ke yaƙi da matsalar tsaron, inda suka riƙa yi masa ihun basa so.
