Shugaban Nijeriya Muhammad Buhari zai gabatar da daftarin kasafin kudin 2021 ga majalisar dokokin ta kasa a ranar Alhamis.
Mai magana da yawun shugaban majalisar dattawa Esrel Tabiowo ne ya sanar da hakan a cikin wata takarda a Abuja..
Ya ce majalisar ta ba da wannan sanarwar ne biyo bayan samun wasika daga shugaban kasa wadda aka karanta a zauren majalisa a ranar Talata.
A makon jiya ne majalisar zartaswar Nijeriya ta amince da kudi Naira tiriliyan 13.08 a matsayin kasafin kudin badi 2021.
