A ranar Alhamis mai zuwa ne ake sa ran shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai gana da gwamnonin Nijeriya kan batun farashin man fetur a ƙasar.
Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya bayyana haka a daren ranar Lahadi bayan taron da aka gudanar tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin ƙwadago a ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa.
Da yake yi wa ƴanjarida bayani kan taron, Ngige ya ce ƙungiyoyin ƙwadagon da kamfanin matatar mai na ƙasa NNPC sun yi bincike kan rahoton sabon tsarin farashin man, tare da bada matsayarsu.
Ministan ya ce ƙungiyoyin ƙwadagon sun nuna gamsuwa kan ci gaban da ake samu, kuma ranar Alhamis Buhari zai gana da gwamnonin kan wannan batu.
