Home Labarai BUK ta soke zangon karatu na shekarar 2019/2020

BUK ta soke zangon karatu na shekarar 2019/2020

263
0

Hukumar gudanarwa ta jami’ar Bayero da ke Kano, BUK, ta amince da soke zangon karatu na shekarar 2019/2020 ga dukkan daliban digiri na farko da manyan digirori.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun magatakardar jami’ar, Fatima Binta-Mohammed.

Cikin sanarwar da DCL Hausa ta samu, jami’ar ta ayyana ranar 18 ga Janairun 2021 a matsayin sabon zangon karatun ga daliban digirin farko, ya yin da kaso na biyu na zangon karatun zai fara a ranar 3 ga Mayu, 2021 ga masu digirin farko.

Su kuwa daliban manyan digirori, kason farko na zangon karatunsu zai fara 18 ga Janairu, 2021, sai kaso na biyu na zangon karatun ya fara a 1 ga watan Juli, 2021.

Daily Nigerian ta ba da rahoton cewa hukumar zartaswar jami’ar ta sauya suna ga zangon karatu na 2019/2020 zuwa zangon karatu na 2020/2021.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply