Home Lafiya Bukatar koyar da darussan magungunan gargajiya a jami’o’i

Bukatar koyar da darussan magungunan gargajiya a jami’o’i

83
0

Hannatu Mani Abu

Shugabar hukumar ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya _NAFDAC_ Mojisola Adeyeye ta shawarci masu magungunan gargajiya a Nijeriya da su hada hannu da ma su binciken kimiyyar zamani ta magunguna wajen bunkasa fannin.

An dai ba da shawarar ne a Abuja babban birnin Nijeriya, ya yin gudanar da taron ma su magungunan gargajiya na nahiyar Afrika na shekarar 2019, da ke da nufin tattaunawa akan hanyoyin bunkasa magungunan gargajiya tare da masu ruwa da tsaki.

Daga cikin dalilan taron, akwai neman saka magungunan gargajiya a cikin jadawalin karatun lafiya a jami’oi a nahiyar Afrika.

Mrs Adeyeye ya yin gabatar da lakca mai taken amfanin hukumar kula da ingancin kaya da magunguna ta _NAFDAC_ da aikace-aikacenta akan bunkasa magungunan gargajiya a Nijeriya wajen tabbatar da ingancin su akan warkas da cutuka.

Ta kuma musanta jita-jitar cewa magungunan gargajiya ba su da illa bisa ga na turawa, ta ce suma su nada ta su illar.

Ta ce Allah ya albarkaci Nijeriya da ganyen magunguna kala daban-daban, sai dai dabarun bunkasa fannin su na fuskantar matsaloli a kasar.

Ta ce idan har aka tashi tsaye wajen habbaka bangaren maganin gargajiya to tabbas za a samu dumbin alfanu ta kuma bukaci masu maganin da suyi rajista da hukumar ta _NAFDAC_

Daga karshe shugabar ta ce idan har aka tsaya ka’in da na’in wajen inganta harkar maganin gargajiya to za a iya samar da kudin shiga ga kasar.

PT: Hannatu/Jani

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply