Tsohon shugaban sojojin ƙasa na Nijeriya, laftanar- janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya bukaci ‘yan Nijeriya su yi watsi da abin da ya kira tsoma bakin ƙasashen waje kan batun wasu takardun da ake danganta su da binciken zargin safarar miyagun ƙwayoyi da ya shafi Shugaba Bola Tinubu sama da shekaru 30 da suka gabata.
Jaridar Punch ta ruwaito Buratai ya bayyana hakan a wata takarda mai taken “Nigeria First: A Case for Protecting National Sovereignty and Dignity”, wadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ya ce bai kamata batun ya lalata martabar Nijeriya ko kuma ya raunana ikon ƙasar na tafiyar da al’amuranta da kanta ba.
Rahotanni sun ce wata kotun tarayya ta Amurka da ke yankin Columbia ta bai wa Tinubu, hukumar FBI da ma’aikatar shari’a ta Amurka wa’adin zuwa 28 ga Agusta 2026 kan yiwuwar fitar da takardun da suka shafi binciken.
Tsohon janar ɗin ya ce batun ya wuce Tinubu kaɗai, domin fitar da takardun na iya shafar martabar Nijeriya da matsayinta a duniya.
Ya ce bai kamata zarge-zargen da ake cewa sun faru shekaru 33 da suka gabata su zama abin da za a yi amfani da shi wajen tantance rayuwar siyasar Tinubu gaba ɗaya ba.
Buratai ya tambayi ko ya dace wata kotun ƙasar waje ta yanke hukunci kan martabar shugaban ƙasar da ‘yan Nijeriya suka zaɓa.
Kazalika ya ce Nijeriya na da hukumomi da tsarin dimokuraɗiyya da ya kamata a bi wajen magance irin waɗannan tambayoyi.
Ya kuma yi gargadin cewa fitar da takardun na iya yin illa ga tattalin arzikin ƙasar, musamman idan masu zuba jari suka ɗauki batun a matsayin alamar rashin kwanciyar hankali.
Inda ya ce hakan na iya shafar damarmakin zuba jari, yawon buɗe ido da sauran harkokin tattalin arzikin Nijeriya daga ƙetare.
Sai dai Buratai ya jaddada cewa bai kamata a kare shugabanni daga bin diddigin ayyukansu ba, inda ya bukaci gwamnatin Nijeriya ta tattauna da Amurka ta hanyar diflomasiyya, tare da kira ga tawagar lauyoyin Tinubu da su yi amfani da hanyoyin doka wajen ƙalubalantar fitar da takardun.
