Home Labarai CBN zai raba asara da manoman da ya ba rancen kudi

CBN zai raba asara da manoman da ya ba rancen kudi

156
0

Babban bankin Nijeriya CBN ya bayyana shirinsa na bayar da kudade ga manoman alkama a kasar domin magance tsadar biredi.

Daraktan bunkasa tattalin kudi na bankin Yusuf Yila ne ya bayyana haka a wani taro da aka shirya tare da manoman rani a Abuja.

Ya ce babban bankin zai raba asara da manoman da suka shiga shirin nan na bayar da rance ga manoma, dangane da asarar da suka yi ta amfanin da suka shuka a daminar bana.

Ya kuma yi kira ga manoman da ke sha’awar noman alkama da su nemo gonaki, ta yadda bankin zai ba su kudaden da za su yi noma.

Yila ya kara da cewa babban bankin Nijeriya zai hukunta duk wani banki da ya ki bayar da kudaden da aka bai manoma karkashin shirin bayar da rance ga manoman kasar nan da babban bankin ya bayar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply