Home Kasashen Ketare Chelsea ta nada sabon manaja

Chelsea ta nada sabon manaja

25
0

Chelsea ta nada tsohon kocin Paris St-Germain Thomas Tuchel a matsayin sabon kocinta kan yarjejeniyar watanni 18.

Tuchel, mai shekara 47, ya lashe kofunan Laliga biyu, da kuma kofin Faransa a cikin shekaru biyu da rabi da ya yi a Paris din.

A farkon makon nan ne dai kungiyar ta sanar da sallamar Frank Lampard bayan ya shafe watanni 18 yana jagorantar kungiyar.

Sabon Kocin dan asalin kasar Jamus Tuchel shi ya zama mai horarwa na 11 da mai kungiyar ta Chelsea Roman Abramovich ya nada tun bayan da ya sayi kungiyar a shekarar 2003.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply