Home Kasashen Ketare China: an yi wa jariri dan kwanaki 66 dashen zuciya

China: an yi wa jariri dan kwanaki 66 dashen zuciya

83
0

[cmsmasters_row][cmsmasters_column data_width=”1/1″][cmsmasters_text]

Abdullahi Garba Jani/dkura

 

 

Asibitin Wuhan da ke lardin Hubei na kasar China ya ce a ranar Alhamis din nan ya samu nasarar gudanar da aikin dashen zuciya ga wani jariri dan kwanaki 66 mai nauyi kilogram 3.

Mahukuntan asibitin da ke hadin guiwa da asibitin koyarwa na jami’ar Huangzhong sun ce wannan jaririn ne mafi kankanta wanda aka yi wa irin wannan aikin a kasar China.

An dai samu jaririn na fama da matsalar zuciya kafin a haife shi a ranar 3 ga watan Afrilu, sai a watan Mayu ne aka yi gwaji aka tabbatar da ciwon. Bayan da aka tabbatar da ciwon ne, likitoci suka tabbatar da cewa yi ma sa dashe a zuciyar ne kadai hanya mafita da za a ceto rayuwarsa.

Likitoci na aiki akan wani jariri

A ranar 8 ga watan Yuni ne jaririn ya samu kyautar zuciya daga wani jaririn dan shekaru 4, da kwakwalwarsa ta daina aiki. Sai da likitoci suka kwashe sa’o’i 5 suna aikin dashen zuciyar ga jaririn.

Shugaban tawagar likitocin da suka gudanar da aikin, Dong Nianguo ya ce ya zuwa yanzu zuciya da huhun jaririn na aiki a hankali, kafin su idasa warkewa duka.

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply