Home Labarai Cikin-shege: ‘Yarsandar da aka kora daga aiki ta shigar da kara

Cikin-shege: ‘Yarsandar da aka kora daga aiki ta shigar da kara

43
0

‘Yarsandar da aka sallama kwanan nan saboda yin ciki ba tare da aure ba, Omolola Olajide, ta shigar da kara inda take neman kotu ta bayar da umurnin mayar da ita aikin ta.

An kori Olajide, ‘yarsanda da ke aiki a ofishin ‘yansanda na Iye-Ekiti, na Jihar Ekiti, a ranar 20 ga Janairun 2021, bisa zargin ta da karya dokar sashi na 127 na dokar aikin ‘yansanda na daukar juna biyu ba tare da aure ba.

A Litinin din nan DCL Hausa ta ga kwafin takaradar “korafin na ta” wanda ta shigar a ranar 3 ga Fabrairu a wata kotun da ke garin Akure, na jihar Ondo, don kalubalantar korar ta.

Ana zayyano rundunar ‘yansanda ta Nijeriya (NPF), da Sufeto-Janar na‘ yansanda (IGP) da hukumar kula da ’yansanda (PSC) a cikin karar a matsayin wadanda ake tuhuma.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply