Home Labarai Cin bashin $22.7bn: Nijeriya na ƙara faɗawa cikin bashi

Cin bashin $22.7bn: Nijeriya na ƙara faɗawa cikin bashi

109
0

Biyo bayan amincewa buƙatar shugaba Buhari na ciwo bashin Dala biliyan $22.7 (6.923trn) da majalisar dattawan Nijeriya ta yi, bashin da ake bin ƙasar zai kai Naira tiriliyan ₦33.078 (108.1bn).

Wannan amincewa dai ta ƙara yawan bashin da ake bin ƙasar na $85.4bn (26.047trn) daga ƙarshen watan Satumbar 2019.

A zaman majalisar na jiya ne dai ta amince da buƙatar Buharin na ranto kuɗin dag ƙasashen waje.

A baya dai Buhari ya aikewa majalisa ta 8 ƙarƙashin jagorancin Bukola Saraki buƙatar ba shi dama ya ciwo bashin don aiwatar da manyan ayyuka tsakanin 2016-2018, amma majalisar ta ce atafau, saboda kasa bata cikakkun bayanai.

Shugabn ƙasar ya sake tura buƙatar a gaban majalisar ta 9 kuma ta amince da shi, bayan rahoton shawarwarin da kwamitin majalisar kan harkokin bashi ya gabatar ƙarƙashin jagorancin Sen. Clifford Ordia.

An samu mahawara mai zafi da ta kai ga farraƙa ƴan majalisar kafin amincewa da buƙatar.

Masana a harkar kuɗi da tattalin arziƙi dai na nuna damu kan ciwo bashin, musamman rashin ci gaban tattalin arziƙi, dogaro da ƙasar ta yi kan fetur da kuma ƙarfin biyan tarin bashin da ke kan ta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply