Home Siyasa Cin hanci na kara ta’azzara a Afrika -kungiyar yaki da rashawa

Cin hanci na kara ta’azzara a Afrika -kungiyar yaki da rashawa

111
0

Transparency international: KUNGIYAR YAKI DA CIN HANCI TA DUNIYA TACE CIN HANCI NA CI GABA DA TAAZZARA A AFRIKA.

A rahoton da ta fitar mai taken ” Global Corruption Barometer ” Kungiyar Transparency International mai yaki da cin hanci a duniya ta ce a duk inda yan Afrika mutum 4 suka hadu to mutum 1 daga cikinsu yana bayar da cin hanci kafin ya samu abinda yake so a maaikatun gwamnati.

Transparency tace irin maaikatu da hukumomi na gwamnati a kasashen Afrika su kan bukaci a basu cin hanci kafin su yi aikin da ya kamata su yi.

Anan Najeriya dai wannan ba sabon abu bane inda ake zargin maaikatan gwamnati da ma wasu shugabannin siyasa kanyi “kashi-mu-raba” da yan kwangila. A wuraren da ake bin layi irinsu asibitoci da sauran wurare, ana zargin jamaan gari kan bayar da cin hanci don a ba su kulawa ta musamman.

Shin ya kuke kallon irin wannan dabia ta wasu jamian gwamnati da jamaar Afrika ganin yadda Transparency tace cin hanci na karuwa?

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply