Home Labarai Ɓangaren shari’a ne kan gaba a matsalar cin hanci a Nijeriya –...

Ɓangaren shari’a ne kan gaba a matsalar cin hanci a Nijeriya – ICPC

96
0

Wani bincike da hukumar yaƙi da cin hanci ta ICPC ta yi ya nuna cewa an bada cin hanci da ya kai ₦9.4bn tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020.

Rahoton ya ce yawaitar cin hanci a ɓangaren shari’a ya ƙaru saboda kuɗin da lauyoyi ke ba alƙalai na toshiyar baki, musamman kan manyan shari’o’in zaɓe da badaƙalar siyasa.

Rahoton mai shafuka 84 ya nuna ɓangarori masu zaman kansu a matsayin na biyun ɓangaren shari’a ga cin hanci, yana mai cewa ɓangaren na taimakawa sosai ga matsalar cin hancin ƙasar.

Rahoton ya ce kashi 9.9% na lauyoyin da aka zanta da su, sun tabbatar da ba alƙalai toshiyar bakin da ta kai ₦5.7bn ga shari’o’in da yawanci na zaɓe ne.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply