Home Addini Batanci ga Musulumci: Gwamnatin Kano ta yi wa UNICEF martani

Batanci ga Musulumci: Gwamnatin Kano ta yi wa UNICEF martani

162
0

Babban lauyan gwamnatin jihar Kano kuma Kwamishinan shari’a Musa Abdullahi Lawan, ya ce kuskure ne ga asusun yara na majalisar ɗinkin Duniya UNICEF, ya ce gwamnatin jihar ta sa baki kan hukuncin da aka yanke wa wani yaro na shekara 10 a gidan yari bisa zargin ta’ba kimar  Annabi (S. A. W).

Wakilin UNICEF a Nijeriya Peter Hawkins ne dai ya yi kira ga gwamnatin jihar ta gaggauta yin duba ga hukuncin, domin soke shi.

Ya ce yanke wa Umar Faruƙ ɗan shekara 13 hukuncin shekara 10 a gidan yari ba daidai ba ne, kuma ya saɓa wa dokar ƴancin yara wanda Nijeriya da jihar Kano suka sa hannu a kai.

Saidai a martaninsa, Kwamishinan shari’ar ya ce babu inda gwamnatin jiha ke shiga tsakani kan hukuncin kotu, kuma batun cewa ƙaramin yaro ne, abun ke rubuce a kundin kotu shi ne, yaron shekararsa 17.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply