Home Kasashen Ketare Corona: Gwamnatin Nijar ta yafe wa ‘yan kasar kudin wuta da ruwan...

Corona: Gwamnatin Nijar ta yafe wa ‘yan kasar kudin wuta da ruwan fanfo

92
1

A wani jawabin kai tsaye ne da ya gabatar ta kafar talabajin kin kasar Shugaba Isufu Mahamadu a karo na biyu a kan batun coronavirus ya bayyana wasu sabbin matakkan da gwamnatinsa ta dauka na dakile yaduwar wannan cuta. A jawabin nasa dai na ranar Asabar da daddare shugaban ya bayyana cewa gwamnati ta dauki matakin karfafa bincike a cibiyoyin kiwan lafiya na kasar dan zakulo mutanen da ke dauke da cutar.

Shugaban ya kuma ce gwamnati ta dauki matakin killace babban birnin na Yamai har tsawan makonni biyu da ke zama daya tillo da aka samu mutanen da ke dauke da cutar an kuma sanya dokar hana zirga zirga daga karfe 7 na yamma har zuwa 6 na safe, dokar da tuni ta fara aiki a wannan Lahadin.

Shugaba Isufu Mahamadu ya kuma bayyana cewa gwamnati ta dauki matakin daukewa masu karamin karfi nauyin biyan kudin wutar lantarki da na ruwan famfo na tsawan watanni biyu masu zuwa.

Ka zalika gwamnatin ta kudiri aniyar saukake ma ‘yan kasuwa haraji a kan duk kayan da za su shigo da su da suka shafi yaki da cutar coronavirus, gwamnatin ta kuma umarci bankuna da su sassauta bada rance ga ‘yan kasuwa masu shigo da kaya daga ketare..

Shugaba Isufu Mahamadu ya kuma bayyana matakin gwamnatinsa na daukar ma’aikatan asibiti 1,500 tare da sallamar firsunoni sama da 1,500.

Ya zuwa yanzu dai mutum 18 ne aka samu masu da cutar ta Covid-19 tare da mutuwar wasu 3 kamar yadda ministan tsaron kasar ya bayyana a wani taron manema labarai da ya kira a safiyar ranar Lahadi a babban birnin Yamai.

Aranar 18.03.2020 ne dai cutar Corona ta fara bulla a kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

Leave a Reply