Home Coronavirus Corona: Katsina ta samu rahoton sabbin kamu 33 a ranar farko ta...

Corona: Katsina ta samu rahoton sabbin kamu 33 a ranar farko ta sassauta dokar kulle

362
0

Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya, NCDC ta ce an samu sabbin kamu daga coronavirus mutum 33 a jihar Katsina a cikin rahotan da take fitar na kowace rana. Rahoton da NCDC din ta fitar da misalin karfe 11 na dare na ranar 18.05.2020 ya ce yanzu jihar Katsina ta na da mutum 281 ke nan.

Hukumar ta NCDC dai ta fitar da rahoton sabbin kamun na jihar Katsina a ranar farko da sassaucin dokar kulle da gwamnatin jihar Katsina ta sanar domin jama’ su shirya wa karamar sallah ya fara aiki. Sai dai NCDC din ba ta bayyana ranar da ta dauki jinin sabbin kamun ba, amma dai babu alamar cewa a ranar Litinin duka mutanen suka kamu.  A bisa al’ada dai gwamnatin jihar kan yi sauri ta rufe duk karamar hukumar da aka bayar da bullar sabbin kamu. Sai dai a yanzu babu tabbas ko gwamnatin za ta janye sassaucin da ta yi a kan dokar a sakamakon sabbin kamu 33 da aka samu.

A yanzu Katsina ita ce jiha ta 4 a cikin jerin jihohin Nijeriya masu coronavirus, Legas ce ta farko mai mutane 2624 sai jihar Kano mai masu corona 842 sai Abuja mai 422 daga nan sai jihar Katsina mai mutum 281.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply