Home Coronavirus Corona: Nijeriya ta samu sabbin kamun da ba ta taba samu a...

Corona: Nijeriya ta samu sabbin kamun da ba ta taba samu a rana guda ba

232
0

Nijeriya ta samu sabbin kamu daga coronavirus mutum 386, adadin da ba ta taba samu a rana guda ba tun a watan Fabrairu lokacin da cutar ta fara bulla a kasar. Lamarin dai ya sa yanzu masu corona sun tashi daga 3,526 zuwa 3,912 a kasar. Alkaluman hukumar yaki da cututtuka ta NCDC ta fitar a ranar Juma’ar ne suka tabbatar da haka.

Hukumar ta ce akalla jihohi 20 sun samu sabbin kamu a ranar Juma’a kuma akasarinsu kafin yanzu da ma suna da masu wannan ciwo.

NCDC ta ce daga cikin mutum 3,912  masu corona a Nijeriya, guda 679 sun warke yayin da cutar ta yi ajalin mutane 117.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply