Home Addini Corona: “shugaba Buhari ba zai je masallacin idi ba”

Corona: “shugaba Buhari ba zai je masallacin idi ba”

237
0

Fadar shugaban Nijeriya ta ce a babbar sallah, Shugaba Buhari ba zai je masallacin idi ba, zai gudanar da sallar idinsa a gida tare iyalansa.

A wata takarda daga Malam Garba Shehu mai magana da yawun shugaban kasa ya fitar, ya ce dama a karamar sallah haka Shugaba Buhari ya yi, saboda dabbaka matakan kariya daga corona.

Takardar ta ce, shugaban kasa ba kuma zai karbi gaisuwar sallah daga bangarori daban-daban ba, kamar yadda aka saba a baya.

Takardar kara da cewa Shugaba Buhari na taya al’ummar musulmi murnar zagayowar babbar sallah.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply