Ranar 6 ga watan Yuni, ita ce cikon kwanaki dari cif-cif da bullar cutar corona a Nijeriya.
Cutar dai ta bulla ne a ranar 27 ga watan Fabrairu, 2020 a birnin Legas ta hannun wani dan kasar Italiya.
Cutar ta ci gaba da yaduwa ya zuwa kusan ko’ina a fadin kasar, in ban da jihar Cross Rivers da har yanzu ba a tabbatar da samun rahoton bullar cutar ba.
Gwamnatoci, kama daga na tarayya zuwa na jihohi, sun dauki matakai daban-daban na dakile yaduwar cutar, ciki kuwa hada rufe wuraren ibada da kasuwanni da takaita zirga-zirga.
