Home Coronavirus Corona ta kama dan siyasar da ya yi murnar mutuwar Abba Kyari

Corona ta kama dan siyasar da ya yi murnar mutuwar Abba Kyari

150
0

Tsohon Kwamishinan Ayyuka na jihar Kano Hon Mu’az Magaji da yayi murnar mutuwar shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa Abba Kyari a shafinsa na facebook shi ma ya kamu da wannan cuta bayan an auna shi. Kodayake daga baya ya fito ya ce ba a fahimce shi bane shi ba murnar mutuwar Abba Kyari ya yi ba.

Hotan sanarwar da Hon Magaji ya rubuta

Hon Magaji shi ne ya fitar da sanarwar a shafinsa na facebook inda ya bayyana cewa ” bayan da sakamakon gwajin da akayi min ya fito daga hukumar kula da dakile yaduwar cutuka masu yaɗuwa NCDC gwajin ya nuna ina dauke da wannan cuta ta Covid-19.”

Idan za’a iya tunawa dai tun bayan kalaman da Hon Mu’az Magaji ya yi Gwamnan jihar ta Kano ya sallame shi daga aiki.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply