Home Coronavirus Corona ta shiga Zamfara, sama da mutum 1000 kuma sun kamu a...

Corona ta shiga Zamfara, sama da mutum 1000 kuma sun kamu a Nijeriya

100
0

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya sanar a ranar Juma’a da daddare cewa cutar coronavirus ta bulla a jihar. Gwamnan ya ce mutum biyu ne a gano a karon farko sun kamu da cutar.

A rahoto na baya-bayan da cibiyar dakile cututtuka ta Nijeriya, NCDC, ta fitar, ta bayyana cewa akwai mutum biyu daga cikin mutum 114 sabbin kamu da coronavirus a kasar.

Alkaluman da NCDC ta fitar a ranar 24.04.2020

Wannan adadin ya kawo masu corona yanzu a Nijeriya sun kai 1095, acewar NCDC. A cikin wannan adadi mutum 208 sun warke yayin da cutar tayi ajalin mutum 32.

Sai dai babu tabbas ko jihar Zamfara ita ma za ta sanar da kulle garuruwa kamar yadda jihar Katsina da jihar Kaduna da jihar Kano a arewacin Nijeriya suka yi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply