Yan siyasa a jihar Nasarawa na fargabar kamuwa da Covid-19 bayan cutar ta kashe dan majalisa.
Gwamnatin jihar Nassarawa ta sanar da rasuwar daya daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar.
Mazauna yankin da kuma ‘yan siyasa a jihar ta Nasarawa na cikin zullumi bayan da Gwamna Abdullahi Sule ya ba da sanarwar cewa, Adamu Suleiman ya mutu a ranar Asabar bayan gajeriyar rashin lafiya.
A cikin sanarwar Gwamnan jihar ya bada tabbacin cewa Coronavirus ce ta yi sanadiyar rasuwar wannan ɗan majalisa.
Akwai kuma fargabar cewa dan majalisar ka iya yada wannan cuta ga wasu daga cikin abokan aikinsa da kuma ma’aikatan kiwon lafiya wadanda suka yi masa magani kafin rasuwarsa.
