Home Labarai Coronaviru: Likitoci sun shiga yajin aiki a Nijeriya

Coronaviru: Likitoci sun shiga yajin aiki a Nijeriya

80
0

A daidai lokacin da kasashe ke daukar matakai daban-daban na yaki da cutar coronavirus, likitoci a birnin tarayya Abuja sun fada yajin aikin sai baba ta gani a ranar Talatar nan.

Kungiyar likitocin ta kasa ARD reshen Abuja sun sanar da shiga yajin aikin ne, kimanin sa’a guda bayan an tabbatar da mutum na uku da ya kamu da cutar a Nijeriya, a jihar Lagos.

Likitocin sun ce sun yi tattaunawa mai tsawo kan halin da ake ciki na barkewar cutar, da yanayin aikin su, da kuma kula da marasa lafiya, kafin su yanke wannan tsattsauran mataki.

A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar likitocin reshen Abuja, Roland Aigbovo ya fitar, ya ce kungiyar ta tafi yajin aikin ne saboda kasawar hukumomin birnin na biyan su albashin su, sama da watanni biyu kenan.

Ya ce wannan ya saka ‘yan kungiyar fadawa mawuyacin hali na matsalar kudade, kuma duk da irin matakan da suka rika dauka na yin gargadi, da bada wa’adi amma hukumomi suka yi biris.

An samu mutum na uku da ya kamu da cutar coronavirus a Nijeriya

A wani bangaren kuma, ma’aikatar lafiya ta jihar Lagos ta tabbatar da mutum na uku da ya kamu da cutar ta coronavirus a ranar Talatar nan.

Kwamishinan lafiya na jihar Akin Abayomi ya tabbatar da hakan ga ‘yan jarida da sanyin safiyar ranar Talata, a sakatariyar jihar.

Abayomi ya ce an kebance mutumin bayan ya nuna alamun kamuwa da cutar, kafin daga bisani gwajin da aka yi masa ya tabbatar ya kamu da cutar.

Duk da cewa mutum uku aka yi zargin sun kamu da cutar, mutum biyu ne aka tabbatar da ita a jikin su, yayin da na ukun bincike ya nuna bai dauke da ita.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply