Home Labarai Coronavirus: Mutum 475 sun mutu cikin kwana guda a Italiya

Coronavirus: Mutum 475 sun mutu cikin kwana guda a Italiya

81
0

Biyo bayan mutum 475 da suka mutu a cikin kwana guda a kasar Italiya, hakan ya sa kasar ta zama inda cutar ta coronvirus ta fi yin illa.

Ko a kasar China dai, inda aka fara samun barkewar cutar a cikin watan Disamba bata samu adadin irin wannan yawan mutanen da suka mutu a cikin kwana guda ba.

A Yakin Lombardy kadai, inda cutar ta fi kamari a Italiya, an samu mutuwar mutum 319 a cikin kwanan guda.

Tun da farko dai kasar ta sanar da kulle gaba daya yankin Arewacin kasar mai yawan mutane miliyan 16 domin takaita yaduwar cutar.

A kasar Iran ma, an samu mutuwar mutum 147 a cikin kwana guda, wanda shi ne mafi muni tun bayan barkewar cutar a kasar, inda yanzu haka yawan mutanen da suka mutu a kasar ya karu zuwa 1,135.

Mataimakin ministan lafiyar kasar ya ce an samu sabbin wadanda suka kamu da cutar 1,192 a cikin kwana guda, wanda ya kara yawan wadanda suka kamu da cutar zuwa 17,161.

Ya kara da cewa Yankin Tehran, shi ya fi yawan wadanda suka kamu da cutar.

a kasar Sifaniya ma, wadanda cutar ta kase ya kaur zuwa 558, yayin da hukumomi suka ce mutum 60 ya kamu da cutar a cikin kwana guda.

Shugaban hukumar bada agajin lafiya na gaggawa, na kasar, Fernando Simon, ya ce yawan wadanda suka kamu da cutar ya karo daga 11,178, da kuma wadanda suka mutu 491 a ranar Talata.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply