Home Labarai Coronavirus: Singapore ta janye ma’aikata 300 daga babban bankin kasar

Coronavirus: Singapore ta janye ma’aikata 300 daga babban bankin kasar

63
0

Kimanin ma’aikata 300 ne aka kwashe daga babban bankin Singapore DBS bayan an gano wani daga cikin ma’aikatan ya kamu da cutar coronavirus.

A baya dai kasar ta bada rahoton mutum 47 da ya kamu da cutar.

Yawan wadanda suka kamu da wannan cuta dai a China ya kai 44,000 yayinda cutar ta yadu a kasashe sama da 20.

An dai yi gwajin ma’aikacin bankin ne a ranar Talata kuma aka tabbatar da ya kamu da cutar a yau Laraba.

Bankin ya ce saboda daukar matakan kariya an kwashe dukkan ma’aikatan dake ginin da jami’in yake, tare da umartar su, su rika gudanar da ayyukan su daga gida.

Baya ga haka an kuma bi diddikin wadanda mutumin ya yi mu’amala da su tare da tsaftace ginin kamar su mahaya, da bandaki don tabbatar da kawar da duk wata yiwuwar yaduwar cutar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply