Home Labarai Coronavirus ta yi illa ga tattalin arziƙin Nijeriya – Buhari

Coronavirus ta yi illa ga tattalin arziƙin Nijeriya – Buhari

121
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koka da cewa cutar coronavirus ta yi illa ga babbar hanyar samar da kudaden shigar kasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Buhari ya yi magana kan yadda cutar ta yi illa ga samar da kudaden shigar kasar, a lokacin da ma’aikatan lafiya karkashin kungiyoyin JOHESU da AHPA suka kai masa ziyara a fadar sa da ke Abuja ranar Talata.

A ranar Litinin ne dai gwamnatin tarayya ta bada sanarwar yiwuwar rage kasafin kudin kasar daga Naira Tiriliyan 10.6 biyo bayan yadda barkewar cutar ya shafi kasuwar man fetur ta duniya.

An kafa wani kwamiti mai wakilai biyar karkashin jagorancin minister kudi da kasafi Hajiya Zainab Ahmed da zai duba yadda za a magance matsalar.

Da yake magana da wakilan JOHESU da AHPA, Buhari ya yi kira ga ma’aikatan lafiyar su yiwa gwamnati uzuri kan bukatun su, a daidai lokacin da take kokarin magance matsalolin da cutar ta haddasa ga tattalin arzikin kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa