Home Lafiya Coronavirus: WHO ta yi gargaɗi kan yin amfani da ibuprofen

Coronavirus: WHO ta yi gargaɗi kan yin amfani da ibuprofen

111
0

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta shawarci duk wadanda suka ga alamun kamuwa da cutar coronavirus, su daina amfani da maganin ciwon jiki na ibuprofen, bayan da hukumomi a Faransa suka yi gargadin cewa yin amfani da magungunan ciwon jiki irin sa suna kara ta’azzara cutar.

Wannan gargadi da ministan lafiya na Faransa Olivier Veran a karshen mako, ya zo ne bayan wani bincike da aka wallafa a mujallar lafiya ta The Lancet, wanda ya nuna cewa shan maganin ciwon jiki irin ibuprofen na kara karfin cutar.

Da aka tambayi mai magana da yawun WHO Christian Lindmeier kan binciken, ya fadawa ‘yan jarida ranar Talata a birnin Geneva cewa masana a hukumar lafiyar na ci gaba da bincike don bada karin shawarwari kan batun.

Saidai kuma ya ce idan har masana kiwon lafiya sun bayyana maganin a haka to tabbas abun da ya kamata a lura da shi ne.

Wannan bayani na shi dai, ya zo ne bayan Veran ya wallafa gargadin yin amfani da magunguna ciwon jikin a shafin sa na tweeter.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply