Home Labarai Covid-19: Ƴan Nijeriya miliyan 11 za su fada kangin talauci

Covid-19: Ƴan Nijeriya miliyan 11 za su fada kangin talauci

106
0

Wani sabon rahoto ya yi hasashen cewa akalla ‘yan Nijeriya miliyan 11 ne za su fada cikin kangin talauci sakamakon annobar Covid-19 nan da shekarar 2022.

Rahoton ya bayyana cewa rukunin ‘yan Nijeriya da ka iya fadawa cikin wannan layin su ne kaso mafi tsoka na mazauna birane wadanda suka dogara da bangaren ayyukan yau da kullum ba wadanda suka dogara da aikin gona ba.

Tun dai kafin annobar COVID-19, an yi hasashen yadda talauci zai mamaye sassa daban-daban na kasar zuwa mutane miliyan 90 nan da shekarar 2022 saboda karuwar yawan mutane a fadin kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply