Home Coronavirus Covid 19: Ƴan Nijeriya milyan 15 suka yi rijistar neman tallafi

Covid 19: Ƴan Nijeriya milyan 15 suka yi rijistar neman tallafi

227
0

Gwamnatin Nijeriya ta yi wa mutane kimanin milyan 15 rijista cikin shirinta na tallafawa masu ƙaramin ƙarfi.

Ministar tallafi da bunƙasa rayuwar jama’a Hajiya Sadiya Umar Farouk ce ta bayyana haka lokacin da take miƙa kayayyakin abinci da ƙungiyar ci gaban ƙasashen yammacin Afirka ECOWAS ta ba Nijeriya ta hannun ma’aikatarta, a Kano.

Ministar ta ce yin rijistar zai ƙara taimaka wa ma’aikatar wajen rarraba kayayyakin abinci ga talakawa mabuƙata domin magance matalar ƙarancin abinci a ƙasar.

Ta kuma ce Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci ma’aikatar da ta taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi waɗanda annobar coronavirus ta shafi neman abincinsu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply