Home Addini COVID-19: An hana bara a Bauchi

COVID-19: An hana bara a Bauchi

94
0

Gwamnatin jihar Bauchi ta ce ta hana yawon barace-barace a jihar don hana yaduwar cutar Corona.

Gwamnan jihar Bala Muhammad yace matakin ya biyo bayan wata tattaunawa da kuma cimma matsaya da aka yi da masu ruwa da tsaki a jihar dangane da barkewar annobar cutar COVID-19.

Gwamnan ya kuma yi bayanin cewa, domin karfafa dokar nan ta jama’a su zauna a gida domin takaita yaduwar cutar Corona Virus yace tuni gwamnati ta kafa kwamitocin da za su yi aiki da shugabannin kananan hukumomi za su jagoranta, tare da hadin gwiwa da shugabannin gundumomi, da na addini da kuma shugabannin tsaro yadda za a tabbatar kowa ya bi doka kamar yadda gwamnatin jihar ta sanya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply