Home Coronavirus COVID-19: El-Rufa’i ya gindaya sabbin sharuddan ibada a Kaduna

COVID-19: El-Rufa’i ya gindaya sabbin sharuddan ibada a Kaduna

1128
0

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i ya saka hannun kan wasu sabbin sharudda da aka gindaya a wajen ibadoji.

Sharuddan sun hada da saka takunkumin rufe hanci, tanadar sinadsrin “sanitizer” da kuma hana cudanya da juna domin tabbatar da an hana yada cutar corona.

A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun gwamnan Muyiwa Adekeye, ta ce sabuwar dokar ta kuma hana taron jama’a kuma sai masu kasuwanci sun samar da na’urar awon zafin jiki “Thermometer” da tanadar dukkanin ababen da ke ba da kariya ga kamuwa da cutar ta corona.

Sanarwar ta kuma ce an takaita yawan masu zuwa ibada, sannan kada lokacin ibadar ya wuce sa’a guda.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply