Home Coronavirus Covid-19: Gwamnati ta gargadi ƴan Nijeriya kan shiga jihar Kogi

Covid-19: Gwamnati ta gargadi ƴan Nijeriya kan shiga jihar Kogi

83
0

Kwamitin shugaban kasa na yaki da cutar COVID-19 a ranar Litinin ya ayyana jihar Kogi a matsayin jiha mafi hadari saboda kin amincewarta na wanzuwar kwayar cutar Coronavirus, da ma yadda jihar ke kin bada rahoto na yau da kullum kan cutar, sannan ta kuma ki samar da cibiyoyin kebe masu dauke da cutar.

Manajan da ke kula da abubuwan da ke faruwa a kasa (NIM) na kwamitin PTF Dakta Mukhtar Muhammad, ne ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa a Abuja.

Mukhtar ya kuma gargadi ‘yan Nijeriya da su kauracewa ziyartar jihar don kada su fada cikin hadari.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply