Home Coronavirus COVID-19: Gwamnatin Gombe ta ba da damar bude makarantu

COVID-19: Gwamnatin Gombe ta ba da damar bude makarantu

185
0

Gwamnatin jihar Gombe ta amince da sake bude dukkanin makarantun gwamnati da ma masu zaman kansu a fadin jihar daga ranar Litinin mai zuwa.

Dokta Habu Dahiru, shi ne Kwamishinan Ilimi na jihar, ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai a Gombe.

Ya ce za a bude makarantun kwana daga ranar Lahadi 4 ga Octoba, yayin da sauran makarantun je ka ka dawo da suka hada firamare da nazare ranar Litinin 5 ga Octoban.

Kwamashinan ya umurci dukkanin makarantun su dauki matakan kariya domin kauce wa bazuwar cutar corona.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply