Shugaban tsare-tsare na kwamitin shugaban ƙasa kan Covid-19 Dr Sani Aliyu ya ce an tura wa jihohin ƙasar Naira Biliyan 50 domin inganta cibiyoyin gwaji da kuma binciko masu cutar.
Dr Aliyu wanda ya faɗi haka a lokacin taron ƴan jarida na kwamitin a ranar Talata, ya roƙi gwamnonin su yi amfani da kuɗin kan abunda aka turo masu kuɗin domin sa ba ga wani abu da ban ba.
Ya kuma jaddada buƙatar da ke akwai na ci gaba da bada ƙarfi har sai an kai cutar ƙasa, yana mai cewa har yanzu cutar na nan da ƙarfinta
