Home Labarai Covid-19: gwamnoni sun amince da hana zirga-zirga tsakanin jihohin Nijeriya

Covid-19: gwamnoni sun amince da hana zirga-zirga tsakanin jihohin Nijeriya

81
0

Gwamnoni 36 na Nijeriya, sun amince da hana zirga-zirga tsakanin jihohin ƙasar na tsawon makonni biyu, domin taƙaita yaɗuwar cutar Covid-19 a jihohin.

Gwamnonin a ƙarƙashin ƙungiyar gwamnonin Nijeriya sun cimma wannan matsaya ne bayan sun saurari jawabi daga gwamnonin Lagos, Bauchi, Oyo da Ogun kan yadda suke yaƙi da cutar a jihohin su.

Wata sanarwar bayan taro da shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Ekiti Kayode Fayemi ya fitar a ƙarshen taron su na shida kan Covid-19 a jiya, ya ce kayayyaki masu muhimmanci ne kaɗai za a riƙa bari suna shiga jihohin.

A taron da aka gudanar ta hanyar tangaraho, gwamnonin sun buƙaci da a faɗaɗa yaƙi da cutar don daƙile yaɗuwar ta, ganin yadda yanzu haka kimanin jihohi 25 ne cutar ta ɓulla.

Sun kuma nuna damuwar ganin yadda aka fi samun ɓullar cutar daga jami’an kiwon lafiya, inda suka ce za su yi aiki da hukumar NCDC domin samar masu da kayyakin kariya da kuma horas da su yadda za su yi amfani da su yadda ya kamata.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply