Home Coronavirus Covid-19: JAMB ta dakatar da ma’aikatanta saboda karya ƙa’idojin kariya

Covid-19: JAMB ta dakatar da ma’aikatanta saboda karya ƙa’idojin kariya

55
0

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta Nijeriya JAMB, ta dakatar da wasu ma’aikatanta biyu da dalibai biyu saboda karya ka’idojin kariya daga cutar Covid-19.

Kamar yadda rahoton mako da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet a ranar Litinin, hukumar ta ce an dakatar da multanen ne bayan wata ziyarar ba zata da magatakardan hukumar Farfesa Ishaq Oloyede ya kai a cibiyar gwaji ta hukumar.

Hukumar ta ce an samu mutanen hudu da karya dokar saka takunkumin kariya dga yaduwar cutar Covid-19.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply