Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa za ta kara farashin kudaden tikitin jirgin kasa da kaso dari ga matafiya da zarar an fara zirga-zirga.
Ministan sufuri Mr Rotimi Ameachi ne ya sanar da hakan a lokacin da ya kai ziyarar aiki a garin Warri na jihar Delta.
Ministan ya ce karin da za a yi ya zama wajibi bisa dokokin da aka sanya wajen daukar fasinjoji.
Mr Rotimi ya kara da cewa a ba ya, kafin bullar annobar corona ko wani jirgin kasa yana daukar akalla mutane 84, sai dai yanzu jiragen za su rika daukar mutane 40 ne kadai.
