Home Coronavirus COVID-19: Ma’aikata za su koma bakin aiki a Kaduna

COVID-19: Ma’aikata za su koma bakin aiki a Kaduna

136
0

Gwamnan jihar Kaduna ya umurci ma’aikatan gwamnati a fadin jihar da su fara fita bakin aiki daga ranar Litinin din mako mai kamawa, bayan shafe kusan watanni 3 suna zaune a gida.

Tun a ranar 26 ga watan Maris din shekarar nan ne gwamnatin jihar ta ba da sanarwar ma’aikatan jihar su zauna gida domin kauce wa yaduwar annobar corona.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa kuma jami’an gwamnati da ke a matakin aiki na 14 da ma na sama da su za su yi aiki a ranakun Litinin da Laraba da kuma Juma’a, ya yin da jami’ai da ke a mataki na 7 zuwa 13 za su yi aiki a ranakun Talata da Laraba kadai.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply