Home Coronavirus COVID-19: Ma’aikatan lafiya 4 sun mutu a Katsina

COVID-19: Ma’aikatan lafiya 4 sun mutu a Katsina

111
0

Gwamnatin jihar Katsina ta ce ma’aikatan lafiya 136 ne suka kamu da cutar corona a jihar tun bayan bullar cutar.

Kwamishinan lafiya na jihar Yakubu Nuhu Danja ya sanar da hakan a Katsina a lokacin taron bita ga ‘yanjarida kan cutar corona.

Ya ce daga cikin ma’aikatan 136, guda 4 sun riga mu gidan gaskiya ta dalilin cutar a jihar.

Jihar Katsina nada yawan mutane 845 da suka kamu da cutar, mutane 364 ne masu dauke da cutar, a ya yin da 24 suka mutu a jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply