Home Coronavirus Covid-19: Ma’aikatan Saudiyya za su koma aiki.

Covid-19: Ma’aikatan Saudiyya za su koma aiki.

137
0

Bayan da annobar coronavirus ta ƙi ci ta ƙi cinye wa a faɗin Duniya, Saudiya ta buƙaci ma’aikatan gwamnati a ƙasar su koma bakin aiki daga ranar Lahadi mai zuwa 30 ga watan Agustan nan da muke ciki.

Wata sanarwa da gwamnatin ƙasar ta fitar daga ma’aikatar kyautata rayuwa da ci gaban al’umma, ta ce ta ɗauki wannan matakin ne bayan samun rahoton da ma’aikatar lafiyar ƙasar ta bayar dangane da samun sauƙi da ake yi wajen bazuwar cutar a fadin ƙasar.

Tuni dai gwamnatin ta bayyana cewa ma’aikatan za su riƙa bin ƙa’idojin da hukumar lafiya ta gindaya domin kaucewa bazuwar annobar, sannan ta yi gargaɗin cewa kada ma’aikatan da za su ci gaba da aiki daga gida su wuce kashi 25 cikin 100 a kowane ofishi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply