Home Coronavirus COVID-19: Mutane 12 sun mutu a Anambra

COVID-19: Mutane 12 sun mutu a Anambra

137
0

Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya tabbatar da mutuwar mutane 12 da aka tabbatar annobar COVID-19 ce ta yi sanadiyar mutuwarsu.

Gwamna Obiano ya sanar da hakan ne ya yin da ya ke yi wa al’ummar jihar jawabi ta gidan talabijin mallakin gwamnatin jihar a daren Litinin, ya kuma bayyana kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen dakile bazuwar annobar corona.

Ya kuma ce zuwa yanzu jihar nada kimanin mutane 101 da gwajin likitoci ya tabbatar da suna dauke da wannan cuta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply